Wednesday, 16 November 2016

Assalamu alaikum Malam wani malamine nake karbar magani awajan sa, to shine naji yafara duba sai nadaina zuwa ko yakamata naci gaba da karba.

Salam alkm mal. Wani malami ne ina karban magani gargajiya gunsa se naji yana duba shin nabar karban maganinsa ko kw?

Waalaikumu salam warahamatulli taala wabarakatuhu

Hakika yakai dan uwa kayi saa domin inasaran kana daga cikin bayin Allah masu nagarta wadanda suke duba wa akan ko maye zasu yi sai sunga no cewa maye Allah madaukakin sarki yafada akan wannan abun, dakuma manzon Allah saw.
Maana masu imani wadanda ke rayuwa akan maganra Allah data manzon sa saw. Kuma domin haka yakamata kowanne musulmi mai imani yazama, dukkan abinda zaiyi
yarika yinsa kan koyarwar Allah da manzon sa.
Duba a harshen hausa yana nufin neman sanin wani gaibi daga cikin abinda yaboyu ga mutum wanda baa San shiba.
Amma a harshen larabci shine ake Kira hisabi Maana lissafi, kamar yadda Allah madaukakin sarki yakawo acikin alqurani cewa :
ﻭﺟﻌﻠﻨﺎ ﺀﺍﻳﺔ ﺍﻟﻨﻬﺎﺭ ﻣﺒﺼﺮﺓ ﻟﺘﺒﺘﻐﻮﺍ ﻓﻀﻼ ﻣﻦ ﺭﺑﻜﻢ ﻭﻟﺘﻌﻠﻤﻮﺍ ﻋﺪﺩﺍﻟﺴﻨﻴﻦ ﻭﺍﻟﺤﺴﺎﺏ .
Maana Allah madaukakin sarki yana cewa:hakika munsanya dare darana su zama ayoyin Allah, sai ubangiji yace sai muka shafe hasken dare muka mayar dashi duhu, amma Ita rana sai muka haska haskenta domin kanemi falalar ubangiji, kuma kusan kirgan kwanaki, dakuma kirgan shekaru. Maana asalin wannan abu da wasu daga cikin maluma sukayi naduba bashine asaliba, asalin abinda Allah yasanya wannan ilimi shine kamar yadda nafada asama. Don haka duba gaskiyar zance babu jaye jaye ko wani gyara da wasu makalkale makalkale babu. Domin manzon Allah saw. Yace dukkan wanda yaje wajan irin wadannan mutane kuma yabada gaskiya daga abinda suka fada yace hakika ya kafirce ma dukkan abinda aka saukar man.
Baduka mai maganin gargajiya bane zaace maganin sa ya haramta domin shima ilimi ne wanda ake koyar sa, kamar yadda wasu sukan gada wajan iyayansu, amma bawai sunayin duba bane, Kokuma wahayi suke samu daga wasu shaidanun aljannu, kamar yadda wannan abun yasami mafaka awannnan zamanin namu.
Akwai wani hadisi wanda yaxo acikin DUBBUN NABAWI. Na Imamu Ibn KAYYUM,cewa wani daga cikin sahabban manzon Allah saw.bayada lafiya sai manzon Allah saw. Yace aje akira Hari's bin kuldah, yazo yana zuwa yace wannan.....
Atare dashi, asamo hulba atafasa aba shi yashi, kuma yasha Allah yabashi sauki take.
Don haka kamar yadda kuka sani shan maganin gargadi ba haramun bane sai dai idan ankai wajen da ya haramta din. Kamar zuwa wajen bokaye da yan bori hakika wannan haramun ne.
Domin manzon Allah saw. Awani hadisi yake cewa babu wata Cuta wanda Allah baisaukar da maganin taba sai dai wanda yasani yasani, wanda baisaniba shine baisaniba. Kuyi magani yaku bayin Allah.
Awani hadisin manzon Allah saw yana cewa acikin ku duk wanda yake da Ikon amfanar da dan uwansa wani abin alkairi da yaaikata hakan. Don haka bil hasalima bada magani wanda yadace da sunnar Allah, da manzon sa to akwai samun lada mai yawa akai.
Wallahu aalam.
Dafatan Allah yakara ganar damu baki daya Ameen.

Monday, 14 March 2016

Assalamu alaikum warahamatullah taala wabarakatuhu.

Dukkan yabo dagodiya sutabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da aminci sutabbata ga manzon Allah sallallahu alaihi wasallam.

Insha Allah wannan shafi zaacigaba dakawo maku bayanai da fatawowi na maluman muslunci, dakuma fadakarwa gwargwadon hali insha Allah.