Guzurin mamaci bayan mutuwar sa!!! Na (3)
************************************
Hadisi ya tabbata acikin Sahihi MUSLIM (RA) daga hadisin #Jarir_dan_Abdullah Yace :Manzon ALLAH saw. Yace:((lallai dukkan wanda ya tabbatar da wani aiki na alkairi kyakyawa acikin muslunci to bashakka yanada lada, da lada ga dukkan wanda Yayi koyi dashi na wannan kyakyawan aikin dakayi, amma batare da antauye ladar wadanda sukayi koyi da shiba, wannan kyakyawan abun alkairin daka aikata ba, aa ladar da zaa baka kaida kafara gaba tar da wannan abun alkairin,ko aikin daban, suma wanda sukayi aiki dashi ladar su daban, domin baa cikin ladar su zaa diba abaka ba na koyin dasukeyi dakai!!!
Haka kuma dukkan wanda yafara asassa wani mummunan aikin nasharri, ko sabon Allah madaukakin sarki, ko wani fasadi to zaa bashi mummunan sakamakon wannan aikin nasa daya kirkira.
Bayan haka kuma zaarika dora masa wani zunubin ga dukkan wanda yayi koyi ko yaaikata irin wannan aikin sharri daka gina ka kirkira, duk wanda yayi koyi dakai abayanka to sai anrubuta maka zunubi kaima akai, tare da cewa zunubin wanda yai koyi dakai daban, kuma zunubin da zaa rubuta maka daban na koyi da sukayi dakai, batare da antauye nasu zunuban ba.!!!!
Ubangiji Allah yamana tsari yakare mu Allahumma Ameen.
Alal hakika ire iren wadannan maanoni na wannan hadisin Antarosu dayawa daga manzon ALLAH saw. Ta fuskoki dadama, Kuma wadanda suke kyawawa,masu inganci.
Sahihi Muslim (3/1255)Babi wanda yake bayani abinda dan adam yake samu na lada bayan mutuwar sa.
Hakika wannan dalili yake nuna mana cewa kan magana na manzon ALLAH saw. Bazaa taba kashe wata rai bisa zalunci ba, face sai Allah madaukakin sarki yadora wani zunubin akan dan adam nafarko wanda yafara sunnanta kisan kai, domin shine wanda yafara gabatar
da wannan mummunan aikin!!!
To idan wannan bayani yakasance tafuskar yin azaba, da kuma ukuba, ko sakamako, to alal hakika abinda yake mafifici akai shine wajan samun falala, da kuma samun lada, ko sakamakon,na irin haka.
Maana idan kafara akata wani aikin sharri to dukkan wanda yayi koyi dakai abayanka to kana da zunubi...... To tunda Hakane wannan yanuna mana cewa kenan ina ga wanda yafara gabatar da wani aiki na alkairi kenan shine yafi cancanta da kuma dacewa asami sakamako.
Wallahu taala aalam.
Ya Allah kabamu Ikon kirkira abin alkairi, ko aiki na alkairi wanda yan bayan mu zasu amfana dashi, domin muma mu amfana dashi koda bayan mutuwar mu Allahumma Ameen.
No comments:
Post a Comment