Wednesday, 1 March 2017

Bayani dangane da abinda yashafi habbatisauda, da kuma manta.

Muujizati Shifaa

Muujizati shifaa :littafin daya tattara bayanai akan yadda zaa iya neman waraka tahanyar amfani da
Habbatirashad
Tafarnuwa
Albasa
Zuma
 
Wanda wani bawan ALLAH balarabe mai suna Abul-fidaa MUHAMMAD azzat MUHAMMAD Aarifi yarubuta.
Allah yasaka masa da alkairi Ameen.

Bayani ko wata hikaya dangane da wani bawan ALLAH wanda Allah madaukakin sarki yajarabce shi da gudawa wanda taki tsayawa har kusan wata (6)wanda yake dayane daga cikin mazauna kasar masar.

Tsira da aminci su tabbata ga shugaban Annabawa da manzanni, shine shugabammu mai sammu mai kaunar mu, kuma abin kaunarmu Annabi MUHAMMAD saw. Tare da Iyalan gidan sa baki daya, da sahabban sa.
************************************

Dafarko abinda wannan bawan ALLAH yafara cewa.......

<<<<<<#Al-habbatisauda_dakuma_zuma>>>>>>

Yace hakika wadannan abubuwan kwara biyu #Habbatisauda da kuma zuma yace wallahi sunada matukar faida da kuma babbar falala da daraja agareni?????????? Badan komai yafadi hakaba sai don tsabar Faidar su daya gani sunyi masa, shi ne yasa shi yake ganin cewa kamar dama don shi kadai aka yo su!!!

Yace nakasan ce nakamu da gudawa mai tsananin gaske har tsawon wata shidda bata yanke ba, yace naje wajen likitocin daban daban suna rubuta man magungunan dake tsayar da gudawa naje nasiyo nasha, amma da zarar nagama sha kafin zuwa wani lokaci sai takara dawowa yadda take kamar bansha maganiba.........

Yace haka naci gaba da kasance wa acikin wannan halin, bayan haka wani likitan gona, kuma masani ta abangaran abinda yashafi jini, da fitsari, shi ma yadebi jini na, da kuma fitsari na domin ya gwada yaga cewa wacce irin cuta ce wanda take haifar man da wannan matsala
Bayan wannan likitan yagama bincike akai sai ya tabbatar da irin matsalar da take daymuna daga nanne nafara jin dadi cewa matsalata tazo karshe!!!

Sai dai akar she wani babban abinda yakara tada mun da hankali shine, bayan dana gama amfani da magungunan daya bani, kawai sai wannan gudawa takara dawowa kamar yadda take!

Nakoma wajan wannan likitan daganan yafada man cewa lallai babu makawa akwai abin lura dangane da uwar hanjin ka, da babban hanjin ka (large intestines) wata kila kodai akwai ciwo aciki ajikin sa, kokuma kuraje acikin ajikin su!!!

Ikon Allah daganan ne babban bakin ciki yasameni, da kuma babbar damuwa wanda tasanya na dimauce, amma duk da haka batasa na yanke tsammani daga rahamar ALLAH ba dangane da samun waraka daga wannan matsalar tawa!

Daganan nafara nazari dakuma tunani cewa kodai naje naga babban  
Likita Dr. Hassan Alhijari, likitan daya kware bangaran Cutuka wadanda baagane kansuba, dakuma bangaran matsalar Ciwon zuciya.

Amma shi wannan likitan yana yima marsa lafiyar sane magani da itatuwa, da kuma ganyayyaki, na muslunchi, da kuma asalin zuma, da hanyoyin neaman waraka wanda mutanan kasar China suke amfani da Ita.
Domin shi baya amfani da magungunan wadanda aka sarrafa su da ainufin chemicals, sai dai lokaci lokaci.

Danaje wajensa sai nadauki kwalbar zuma, yana kallona sai yace ga maganin ka nan a hannun ka kana rike dashi!!!

Kabar magani a gefen ka kana ta wahala kawai!!!

     Daga gobe na hore ka da kasha karamin kofin zuma dukkan bayan awa (3)haka zaka cigaba da yi har zuwa kwana daya.

Bayan haka sai kasamo #Huran_albabunaj katafasa sai katace kazuba cokali daya na zuma kasha kafin kaci abinci daawa daya...... Ikon daganan sai naji nafara samun yanayi mai dadi lafiya tafara samuwa kadan, amma dai wannan gudawa bata tsayaba baki daya.


Daganan sai wani abokina yabani wannan littafin mai suna ((Muujizati shifaa))

 
Daganan kawai sai gashi nasami abinda nabata acikin sa wajen neman sa, Yace sai nasamo man #Habbatisauda kawai kai tsaye nakama yin magani dashi,kamar yadda aka fada acikin wannan littafin, daganan cikin Ikon Allah gudawa tatafi baki daya bayan kwana uku dafara amfani da man habbatisauda,wanda yake na kwashe sama da wata biyar inafama  da Ita bata tsayaba.

Yace :Daganan nacigaba da cin kowanne kalar abinci, nasami lafiyar jikina fiye da shekarun da suka gabata.

Yace alal hakika bazan iya suffan ta irin yadda habbatisauda tazama magani mai ban mamaki wajan magance mun dukkan rashin lafiya ta ba.

Yace wannan abinda najarraba, don haka nabada ta sadaka ga dukkan wani mara Lafiya wanda yarasa magani daga Ciwon sa bayan duk yayi iya bakin kokarin to ga hanya sadaka. 

Yace Allah shine wanda yake me tabbatsr da shaida akan abinda nafada. 

Dafatan ALLAH yasaka masa da alkairi Allahumma Ameen. 

Rahamaniyya Islamic medicine Centre Funtua. 

Twitter @likitanci. 

Whatsapp 08152753609.

rahamaniyyaharbalmedicine.blogspot.com

No comments:

Post a Comment