Wednesday, 1 March 2017

Guzurin mamaci bayan mutuwar sa kashi na (4)

Manya manyan dalilai da suka zo daga cikin alqurani, da sunna  da ijmain maluma, da kuma kawaid na Sharia wadanda suke nuni akan wadanda suke mutu suna samun lada tahanyar ayyukan wadanda suke raye......

Kamar Allah madaukakin sarki yafada acikin suratul hashar aya(10)

Allah madaukakin sarki yace "wadannan wadanda suke biyo bayansu suna cewa ya ubangijin mu kayi mana gafara, tare da yan uwan mu wadanda suka rigaye mu wajan yin imani...... "Allah yana yabon mu tahanyar yima bayin Allah wadan da suka riga mu yin imani tun farko ,sune sahabban manzon ALLAH saw. Domin haka manzon ALLAH saw. Yafada fiyayyun alumma sune wadanda sukayi zamani dani..... To wannan dalili yanuna cewa dalilin rigayar mu imani shi yasa ubangiji yasanya suna amfana da istigfarin mu, da kuma neman gafara da muke yi muna hadawa dasu aciki.
والذين جاءوامن بعدهم ربنااغفرلنا ولاخواننا الذين سبقونا بالإيمان....... الا ية.
Don haka indai kayi istigfari to suma suna da nasu rabon aciki na abinda suka kafa na alkairi, kuma nasu ba zai sa atauye nakaba.

Kamar yadda maluma sun tattaru basuyi sabani ba wajan yima mamaci aduah tahanyar roka masa gafara alokacin daake yima sa SALLAH.

Hadisi ya tabbata daga sunan na Abu Dawud (rahimahullah) Daga hadisin na Abu huraira (RA) yace :manzon ALLAH saw. Yace ((Idan zaku sallaci mamaci to kukebanta wajan yi masa addua,tahanyar roka masa gafara.

Bayan haka Anrawaito wani hadisi acikin Sahihi Muslim daga hadisin Aufi dan MALIK (ra) yace:wata rana manzon ALLAH saw. Yanayin sallatar wata gawa, sai muka kiyaye wani abu daga cikin adduoin dayarika yi, yana cewa "((Ya ubangiji  kayi gafara agare shi, kajikan sa, kayi masa rangwame, ka kuma saukaka masa, ka girmama masaukin sa, ka yalwata masa shi, kawanke shi daga dukkan zunubai, da ruwa, da kankara, da sanyi ka kuma tsarkake shi daga kurakuransa daya aikata sukoma fari fat,kamar yadda muke wanke farin tufafi daga datti, kuma ka canza masa gida wanna yafi gidan sa na duniya, ka canza masa Iyalan sa fiye da iyalinsa dayabari a duniya, ka canza masa mata fiye da matar sa ta duniya, ya Ubangiji muna rokonka kashigar dashi aljanna, kayi masa kariya daga azabar kabari.

Dafatan ALLAH ubangiji yayafe mana dukkan kurakuranmu zahiri ,da badini, Ya Allah ka kyatata karshen mu kasa mucika da imani. Ka gafar ta ma dukkan mamatan mu musulmi maza da mata Allahumma Ameen.

No comments:

Post a Comment