Tuesday, 6 June 2017

Azumi yana daga cikin rukunnan muslunci kwara (5)

Alal hakika kamar yadda kuka sani azumi yana daya daga cikin rukunnan muslunci,kuma wajibi shi,domin yana daga cikin abubuwan wadanda muslunci ya wajabta.

Allah swt.yana fada acikin suratul bakra"Yaku masu imani hakika mun wajabta yin azumi akan ku kamar yadda muka wajabta shi ga alummar dasuka gabace ko kun kasance masu jin tsoron Allah.ayah(183)

Allah swt.yakara da cewa "Watan Ramadan shine wata wanda aka saukar da alqurani acikin sa domin yazama shiriya ga jamaa,da kuma hujjoji na shiriya da rarrabewa tsakanin abinda yake dai dai,da kuma wanda ba dai dai,tsakanin bata da kuma shiriya,tsakanin gaskiya,da kuma karya.....yakara da cewa dukkan wanda ya halarci wannan wata yana mai lafiya,yana mai hankali,kuma wanda yake baligi to ya azumce shi.bakra ayah(185).

Ansamo wani hadisi daga dan Ummar (ra)yace:Manzon Allah saw.yace:((Angina addinin muslunci ne abisa abubuwa kwara (3)

(1)Mutum ya shaida babu wani abu da ya cancanta a bauta masa sai Allah swt.shi kadai.

(2)Shine dole ka tabbatar cewa Annabi Muhammad saw.Manzon Allah ne.

(3)Kuma shine tsayar da sallah,maana kabatar da sallolin farilla.

(4)Da kuma bayar da zakka.Ga wanda Allah swt.yaba shi iko,da hali.

(5)Ziyartar dakin Allah,da kuma azumtar watan Ramadan.

Ansamo wani hadisi daga Abu huraira (ra)Yace:manzon Allah saw.Yace:Dukkan wanda ya azumci watan Ramadan yana mai imani,da kuma kyatata zaton sa ga Allah to Allah zai gafarta masa zunubansa da suka gabata.

Anrawaito wani hadisi shima daga Abu Huraira (ra)yace:Hakika maaikin Allah tsira da aminci su tabbata agare shi yace:Allah mai girma da daukaka yace:Kowanne aikin lada wanda dan adam zaiyi to nasane wannan,amma banda azumi,azumi wannan nawane,nine zanbada sakamakonsa da kaina.Azumi kuma kariyane,kuma garkuwane,yace idan aka wayi gari dayan ku yana azumi to kada yarika yin maganganu na alfahsha,maganganu marasa amfani,kada yarikayin ayyuka marasa amfani,ko wasanni marasa anfani,yace idan wani mutum yazage ka alhali kana azumi,ko yanemi da fitina,ko yane meka da fada to kace masa ni azumi nike,ka mai maita masa hakan har sau biyu.

Yace narantse da wanda rayuwata take a hannunsa yace warin bakin mai azumi awajan Allah ranar alkiyama yafi kam shin Almiski,kuma mai azumi yana da abubuwan farin ciki kwara biyu,wadanda zaiyi farin ciki dasu:Sune Alokacin da yayi buda baki zaiyi farin ciki da haka,bayan haka kuma da lokacin da ya hadu da  Allah swt.nan ma zai yi farin ciki da wannan azumin da yayi.

Domin akwai wani hadisi daaka samo daga Sahal dan Saad (ra)Yace:Hakika manzon Allah saw.yace acikin aljannah akwai wasu kofofi anace masu rayyan,wadannan kofofi masu azumine kadai zasu shigesu aranar alkiyama,babu wani mutum daya da zaa bari ya shiga wanda ba mai azumi ba.Yace zaarika yin kira ana cewa .......Ina masu azumi...ina masu azumi?Daganan zasu tashi babu wani mutum daya da zaa bari ya wuce wannan kofa sai su kadai kawai,kuma da zarar sun gama shiga sai arufe kofar bawanda zaa bari yakara shiga daga nan.

Ya ubangiji kasa muna daga cikin wadanda zasu shiga wannan kofar ameen.

No comments:

Post a Comment