Wednesday, 7 June 2017

MENENE HUKUNCIN WANDA YACI ABINCI,KO YA SHA ABIN SHA DARANA ACIKIN RAMADAN BISA GA MANTUWA?

Alal hakika wajibine kamewa acikin Ramadan tun daga bullowar alfijir,har zuwa lokacin da rana zata fadi.

Kamewa daga ci,da sha,da kuma yin jimai awannan lokacin,dadai sauransu.

To menene hukuncin wanda yaci,ko yasha acikin ramadan da rana bisa ga mantuwa amma daga baya ya tuna.Bisa ga zance mafi inganci daga bakin maluma shine,idan mutum yaci,ko yasha acikin watan ramadan da rana da gangan to wannan sai yayi kafara azumi (60)Ajeri sannan kuma yarama dayan.

Amma idan bisa kuskure ne to akace babu laifi,maana bazaiyi koda ramuwa na wannan azumin,kuma bazaiyi kaffara ba.Saboda akwai hadisin daaka samu daga Abu huraira (RA)yace:Manzon Allah saw.yace :"Dukkan wanda yamanta cewa yana azumi sai yaci,ko yasha to yacika sauran azumin,maana yaci gaba yakai wannan azumin,domin Allah ne yaciyar dashi,kuma yashayar dashi"

Bayan haka jawo amai da gangan,shima yana karya azumi,amma wanda amai yarinjaye shi batare da son ransaba to akace wannan babu laifi akansa bazai ramuwar wannan azumin ba,kuma bazai yi kaffara ba.

Ansamo wani Hadisi daga Abu hurara(RA)yace :Hakika manzon Allah saw.yace "Dukkan wanda amai ya gangaro masa hakanan to babu ramuwa akansa,amma dukkan wanda ya kakalo shi da gangan to yarama wannan azumin.

Bayan haka Jinin haila,da kuama jinin haihuwa koda koda gab da zuwa karshen yinine maana saura kadan rana tafadi sai yazoma mai yin azumi,bisa zancen maluma mafi inganci to wannan azumin babu shi,sai dai ayi ramuwarsa.

Yaku yan uwa hakika dukkan wanda Allah swt.ya hore masa yalwa to yakamata yarika taimakon wadanda suke da rauni basuda abin zasu anjima balle na gobe,domin wannan lokaci lokaci mai tsada,domin ciyarwar acikin watan ramadan,ko kuma bayar da sadaka yafi lada bisa ga kowanne lokaci,kuma yin hakan yana daga cikin abinda Allah swt.ya umar ce mu da yinsa,domin haka yake fada ma dan karuun cewa "Ka kyatata ma alumma kamar yadda Allah ya kyatata maka tahanyar baka wannan wadatar,kada kazama mai yin fasadi abayan kasa,domin Allah bayason mai aikata fasadi wanda yake mabar naci"(Suratul kasas).

Wallahu taala aalam.

Ya Allah kayafe mana dukkan zunuban mu wadanda muka aikata su muna sane,da kuma wadanda muka aikata batare da munsan cewa mun aikata suba,ya Allah kasa muna daga cikin bayinka wadanda zaka yantar dasu daga shiga cikin azabar ka aranar alkiyama,ya Allah kabiya mana dukkan bukatunmu na alakairi,marasa lafiya ya Allah kabasu lafiya muda muke da ita ya Allah kakara mana ita,shuwagabbanin mu ya Allah kataimakesu kabasu ikon yin adalci agare mu,ya Allah kabama shugaban kasar mu lafiya,domin albarkacin sunayan yahayyu ya kayyumu ameen.

Dukkan abinda kukaga mun kawo anan to yananan acikin shafinmu mai suna
FATAWOWIN MAGABATA
Idan kuma kuna bukatar bincikowa kai tsaye to zaku iya rubutawa akan Google kai tsaye,kokuma ta wannan address dake kasa.
musluncitafarkintsira.blogspot.nl/?m=1


Tuesday, 6 June 2017

Fatawowin magabata

musluncitafarkintsira.blogspot.nl/?m=1

MACE MAI CIKI,DA KUMA WANDA TAKE SHAYARWA.

Mace mai ciki,da kuma wanda take shayarwa maluma sukace idan bazasu iyayin azumi ba,kokuma suka ji tsoro ga yaronsu to suci abinci,amma zasu bayar da  fansar wannan azumin,kuma babu ramuwa akansu.

Ansamo wani hadisi daga dan Abbas (RA)yace:((Anyi rangwame ga wanda yake tsoho,da kuma mace  tsohuwa awajan wannan,amma abinda yake akansu shine suci abinci kuma suciyar akowacce rana zasu ciyar miskini.Babu ramuwa akansu.wanda yake ada koda tsoho ko tsohuwa zasu iyayin azumi idan sunso suyi azumi,idan sunso suci abinci,sai suciyar da miskini akowacce rana sai aka shafe wannan da fadin Allah swt.cewa (Duk wanda yazama watan Ranadan yakama yanada cikakkiyar lafiya,da hankali,kumA baligi yazama wajibi yayi azumi))

Amma sai akayi rangwame ga mutumin dayake tsoho,ko mace tsohuwa idan basa iya yin azumi,da kuma mace mai ciki,da kuma wanda take shayarwa idan sunji tsoron cutarwa ga yayayan su to akace suci abinci,amma kowacce sai suciyar da miskini.

Bayan haka da kuma wani Karin bayanin daga dan Abbasu (RA)Yace ((Idan mace mai ciki taji tsoro akanta kada tasha wahala mai tsanani,da kuma mace mai shayarwa taji tsoro ga yaronta kada kada yasha wahala acikin watan Ramadan tahanyar rasa nonon da zai sha sai yace:to ya halatta suci abinci,kuma suciya da miskinai akowacce rana,kuma bazasu rama wannan azumin ba.

Ansamo wani hadisi daga Nafiu(RA)yace:((Wato yakasance wata diya daga cikin yayan dan Ummaru (RA)tana karkashin wani mutum bakurai she,kuma yazama tanada ciki acikin watan Ramadan,sai kishi yasame ta acikin wannan wata,kishi matsananci,sai dan Ummar ya ummar ceta dacewa taci abinci,kuma taciyar da miskini akowacce rana))

Wallahu aalam.
Ya Allah kagafarta mana zunubanmu gaba daya,kayi mana rahma,kabiya mana bukatunmu na alkairi ameen.

Yana daga cikin nauikana shirka na bokaye,dabkuma Arrafa,malamai yan duba!!!

Boka,da kuma malaman duba maganar gaskiya dukkansu sun kafurce ma Allah swt.saboda sunyin daawar sanin gaibi,abinda yake aboye ko zai faru jibi,nanda sati,shekara,ko shekaru,domin hakika sanin gaibi sai Allah.

Duk da cewa wasu maluma sukan kasa sanin gaibi kala daban,kamar alal misali Allah yakan sanar da annabawa wasu alamura ta hanyar wahyi daake yi masu.da dai sauransu.

Amma mafi yawa daga cikin gaibin da yan bori,da bokaye,da malaman duba suke daawar sanin sa badole bane yazama gaskiya,da yawa sunayin dubaru domin amsar kudin jamaa ne kawai wadanda suka rafkana,ta hanyar zana alkaluma,ko bugun ramli,kokuma duba hannun mutum,ko azuba ruwa a koko ko kwalba da sunan ganin matsalar mutum,koko madubi,da dai sauransu.

Domin bugun kasa duk da cewa irin harrufan alqurani ne ake bugawa suzama harrufa,to wannan ba dalili bane nayin haka,saboda ba shine manufar sanar da wannan ilimin ba,domin Allah swt.yace mun sanya ilimin hisabi ne,ba don ayi dubaba sai don kusan yawan kirgan shekaru,da kwanuka,da watanni.

Amma yanzu sai kaga anmai da abun sanaa,yanzu idan mutum yaje wajen neman magani,ko wata bukata in har wannan bokan,ko dan duban,ko dan bori bai iya wadannan dubarun ba,to bazai sami ko mai ba.......saboda tsabar imani da wasu daga cikin alumma dasukayi da hakan.

Kuma inda babbar illar take shine zaka gani sukan fahimci cewa menene kake so,to koda sunga cewa wannan abun ba zai yiwuba to bazaa taba fada maka hakaba,domin idan anfada maka gaskiya to bazaka bada kudi da yawaba,wannan dalili sai yasa afada maka karya domin kabada.

Kokuma koda anga cewa wannan bukata taka babu wata matsala zata yiwu sai ace kai ai dole sai anyi aiki akai,nanma afada maka karya kawai don a amshi kudinka,to wannan kuma ya shiga cikin saba ma Allah,domin yin karya haramunne a muslunci.Kaga daganan ata dalilin neman duniya mutum yazama makarya ci karfi da yaci.

Akwai wani babban mutum awannan kasar tamu da zan fadesa kowa zai san shi,domin yasami matsayi kala daban,daban wajen aiki,awani lokaci sai ya fito takara kuma yasa aka tara masa malamai irin wadannan masu yin duba din!!!

Kowa da ya buga kasa sai ai zaayi nasara babu makawa zai ci wannan zaben.
Sai wani malami shi kadaine yace aa gaskiyar magana babu nasara akan wannan tafiya,domin bazai ci wannan takaraba,yace kai karya kakeyi dukkan wadannan maluma kowa yace zaayi nasara sai kai kadaine zakace ba zaayi nasaraba,wannan ba gaskiya bane.

Saura aka basu buhunan shinkafa,da kudade masu yawa aka sallame su suka tafi.

Shi kuma da yace bazaayi nasara hakanan yata shi yatafi.
Anan nan anata yin kamfe akazo wajen yin zaben yan labai yafadi baiciba!!!Nan take yagane cewa sauran wadannan maluman karya suka fada masa kawai domin yabasu kudi.
Wannan dayan shi kadai ne yafadi gaskiya.

Domin manzon Allah saw.yace dukkan wanda yaje ma mace wanda take jinin haila maana yasadu da mace mai yin jinin haila,da kuma wanda yasadu da mace ta duburarta,da kuma wanda yaje wajen boka to yakafurta da abinda ka saukar agare shi.Allah yakare mu ameen.

Domin boka ko dan bori,ko malumin duba idan yafadi gaskiya sau daya to sai yayi karya sau( 99)Amma mutanen da suka rafkana zuciyar su ta dusa she bazasu gane hakanba.

Domin mutane suna zuwa wajen su domin sanin abinda zai faru agaba,da abin farin ciki,da kuma abun bakin ciki,imma tahanyar aure ko kasuwa,da bincike akan abinda yabata da dai sauransu.

Sannan kuma mutane sukan gaskta abinda aljannu suka fada abakin bokaye ko yan bori.Bil hasalima yanzu idan kana bayar da magani awajen wasu indai bawai kana da wasu shaidanun aljnnu dake ma wahyiba to basu dauka cewa kasan wani abu.Allah yakyata ameen.

Ban mantawa akwai sanda inayima wata baiwar Allah Ruqqa sai wannan  aljanin yace ai shi yana kareta ne ,badon haka da abun yayi tsanani sosai!!!Sai nace masa kai wayake kareka yace Allah,nace to itama Allah ne yake kareta.......kuma nanu na masa hakan amma yakasa ganewa.

Daga nan nace masa tunda kaki yarda da abinda nafada to yanzu kasan abinda zai faru dakai anjima da yamma?yace aa,sai yace ai kaima baka saniba,nace masa dama kaji nace maka nasan abinda zai faru danine nanda anjima.

Nace masa dama kai da kake cewa kana kareta to kai kanka bakasan cewa menene zai faru dakai nanda anjima ba to tunda kau hakane to ta yaya zaka iya kareta.

Amma malamai sunce kamar alal misali wanda yatafi wajen su domin yin gwaji,amma shi bai gaskata suba cewa sunsan gaibi,amma yana zuwa domin ya gwada yagani,da dai sauransu to wannan airin haka bai zama kafuri ba,amma sai dai bazaa karbi sallar saba ta kwana (40)Dalili kuwa shine fadar maaiki saw.cewa dukkan wanda yaje dan duba ya tambaye sa akan wani abu,to bazaa karbi sallar saba har ta kwana (40)Tare da cewa wajibine kuma yaci gaba da yin salla,kuma yana tuba zuwa ga Allah swt.

Wallahu taala aalam.
Ciyarwa acikin watan ramadan ta hanyar dafa abinci abayar da sadaka,ko kuma taimaka ma bayin Allah abasu sudafa da kansu yanada lada mara iyaka.Domin fadin Allh swt.acikin suratul bakra.cewa:(Misalin mutunen da suke ciyar da bayin Allah don Allah,to kamar misalin mutumin daya shuka kwara dayane ta dawa,ko masara,ko gero,wannan kwara dayan daya shuka tafito tayi tushe (7)kuma kowanne tushe yayi kwaya dari ba kwai(700)To kamar hakane ubangiji yake rubanya lada ga wanda yaciyar domin ko yabayar da sadaka,kuma Allah swt.yace yana kara rubanyawa ga wanda sama da (700)din ga wanda yaso))
Ya Allah kabamu abinda zamuyi,kuma kabamu ikonyi ameen.

ABINDA YAZAMA WAJIBI AKAN WANDA YAKE TSOHO TUKUB TUKUB,DA MACE WANDA TAKE TSOHUWA TUKUB TUKUB,DA KUMA MARA LAFIYA WANDA YAKE WANNAN RASHIN LAFIYAR TASA BAA TSAMMANIN SAMUN WARAKA,MAANA ZAI WARKE DAGA ITA!!!

Zance mafi inganci inji maluma shine,duk wanda yazama yagajiya saboda tsufa baya iya yin azumi Ramadan,ko makamancin hakan to zai ci abinci,amma ana bukatar kuma kowacce rana sai yaciyar da miskini,saboda fadar Allah swt.((Cewa ga wadannan wadanda basa iya yin azumi,maana yin sa hakan zai sa susami wahala kwarai to zasu rika bada fidya kullum shine ciyar da miskini.))Bakara aya(184).

Ansamo wani hadisi daga Adain cewa yace yaji daga Dan Abbasu (RA)Yaji ana karanta wannan ayah((وعلي الذين يطيقونه فدية طعام مسكين))Sai dan Abbas (ra)yace:Wannan ayah baa shafe hukuncin taba,abinda take nufi maana shine tana nufin tsoho tukub,da kuma mace tsohuwa tukub,idan basa iya yin azumi,to abinda zasuyi shine kowacce rana sai suciyar da miskini.

Sahihul irawaa(912) Kuma wannan hadisi danganensa ingantacce ne daga ibni Jareer.(135/2)

Hakika wannan lokacine nasamun lada,don haka dukkan ibadar da kayi zaa ninka ma ita ne,don haka wanda Allah swt.ya hore masa dama da hali,to yatai maki bayin Allah gwargwadon iya warsa.

Domin awani Hadisi manxon Allah saw.yana cewa duk wanda yaya ye ma wani muimini wani bakin ciki daga cikin bakin cikin duniya,to Allah zai yaya ye masa bakin cikin duniya da lahira.

Domin ayyukan shiga aljannah basuda iyaka,bakasan cewa wanne aikine zakayi wanda zai kaika zuwa ga aljannah ba,domin dukkan ayyukan samun lada babu abinda yakai ciyarwa lada,ko shayarwa.

Dafatan Allah yabamu ikon yi ameen.
Wallahu taala aalam.

WANNE YAFI GA MATAFIYI,DA KUMA MARA LAFIYA SHIN CIN ABINCI NE YAFI,KOKO YIN AZUMI?

Malamai sukace idan mara lafiya,ko wanda yake matafiyi yazama bazai samu wahala ba ata dalilin wannan azumin da zaiyi ahalin rashin lafiya,ko halin tafiya to yin azumi shi yafi.

Amma matafiyi,ko wanda yake mara lafiya yazama cewa idan sukayi azumi zasu sami wahala to maluma sukace a irin wannan hali cin abinci shine yafi.

Domin ansamo wani hadisi daga سعيد الحذري رضي الله عنه.
Yace:((Hakika mun kasance muna tafiya zuwa yaki alokacin watan Ramadan tare da manzon Allah saw.acikin akwai masu yin azumi,akwai kuma wadanda basa yin azumi maana suna cin abinci,domin kada su sami mushaqqa.
Kuma ahalin hakan wani baya damuwa da wani,maana mai yin azumi bai da dan uwan saba saboda baya yin azumi,shima wanda baya yin azumi bai damu da cewa suwane ai suna azumi ba,ahakan shima ranar da yaga yasami karfin jiki sai yayi,randa yaga yasami rauni sai yaaje domin hakan shine mafi kyawu.

Wallahu taala aalam.

YANA DAGA CIKIN NAUIKA NA SHIRKA WADANDA SUKA WATSU KO INA,KUMA ZUKA BAZAMA KO INA AWANNAN ZAMANI NAMU,LUNGU DA SAKO,BIRNI DA KAUYUKA.

Sune kamar haka:

(1)Nafarko shine yin Sihir.
(2)Nabiyu kuma shine Bokanci.
(3)Shine arrafa maana Yan duba.

Alal hakika yin sihir kafurcine,domin yana kafurta mai yinsa domin yana daya daga cikin abubuwa kwara (7)wadanda maaiki Allah tsira da aminci yace Allah ya gaggauta ukuba ga masu yinsa,domin sihir yana cutar wa,baya da amfani((Domin Allah madaukakin sarki yana cewa suna neman sanin abinda zai cutar dasu,kuma bazai amfane suba))Suratul bakara (102)Bayan haka Allah swt.yace :Masu yin sihir bazasu kubuta ba takowacce fuska.Dahaa ayah(79)

Bayan haka mai yin sihir ya tabbata kafiri domin Allah swt.yana cewa((Annabi Sulaimana (As)bai kafurtaba,sai dai Shaidanune suka kafurta domin sune suke koya ma mutane yadda akeyin sihir,Allah swt.yace kuma babu abinda aka saukar akan wasu mutane kwara biyi haruta,da marut,balantana har su koyar da wani mutum daya sihir,sannan suce masa mufa fiti nane,don haka kada ka kafurta)).

Hukuncin mai yin sihir,shine kisa bisa zancen maluma,kuma dukiyarsa haramunce.

Don hakane zakaga daga cikin wasu jamaa wadanda suke jahilai,ko kuma azzalumai,ko wadanda suke masu raunin imani,suna zuwa wajan masu yin sihir domin suyi masu sihir,domin su aikata wani mummunan aikin taadanci akan wasu bayin Allah,ko kuma daukar fansa.

Akwai kuma wadanda zaka ga suna zuwa su aikata wata alfahsha,koko wani aiki wanda Allah ya haramta tahanyar dalilin zuwan su wajen wannan mai yin sihir din,ko don warware sihir,ko kuma neman duniya,ta hanyar jefa mutane cikin zinace xinace,ko aikata manyan kabair,kamar yin luwadi da sunan samun duniya,kokuma kashe rai duk da sunan neman duniya,domin balain da mai sihir yake haifarwa yafi balain daake haifar wa agidan giya.

Kokuma war ware sihir,ta hanyar sihir wanda wannan badai dai bane,domin baa warkar da cuta da cuta,sai dai awarkar da cuta da magani,tahanyar komawa ga Allah swt.da neman waraka agare shi,tahanyar karanta alqurani da dai sauransu.

Bana mantawa wani abin tada hankali,kuma babban balin da ya zama ruwan dare ayanzu ubangiji Allah yamana tsari kuma shikare mu ameen.

Wato akwai wata baiwar Allah da mai gidanta yake shirin kara sabon Aure,kuma yake dauko wanda zai aura din yana kawota har gida,har wata rana takira wannan matar tasa take ce mata wlh.idan nashigo wannan gidan dole sai kinbar shi,hakan yatada mata da hankali,hakan yarika jawo matsala a tsakanin ta da mai gidanta,akoda yau she sai dai nanuna mata girman  Allah,da kuma tayi hakuri,tayi fatan alkairi,kuma tagaya ma ubangiji da muwar ta,har nace nima zan tai maketa da aduah akan samun zaman lafiya.........Ashe gaba daya hakan bai gam she taba......wlh har sai da aka wayi gari wata kawar banza tajata takai ta wajen wani makiyin Allah,da manzon sa saw.

Sai tafada masa dukkan da muwar ta akar she shine ya ummar ceta da cewa ta kwabe kayan jikinta duka saboda akwai maganin da zaayi mata,amma sai yaduba jikinta tukunna......Ya Allah kakare mu daga sharrin zamani ameen.

Bayan sundawo ne takirani take shai da man cewa itafa tayi wani abu amma bata san yazata yiba,bata san yazatayi tatubaba tafa she da kuka.........Daganan taka she wayarta,tun safe har zuwa yamma,daganan takara kirana tace wallahi malam wata kawata takai ni wajen malami ashe boka ne ban saniba,yace man nayi kaza da kaza.......Daganan takara fashewa da kuka!!!

Inna lillahi wainna ilaihi rajiun.
Daganan jikina ya hau bari,zuciyata takama makyarkyata.

Tace yanzu don Allah malam yazanyi natuba?Nace mata abinda yace kiyi kinyine tace aa,nace indai har bakiyi abinda yace kiyiba to da sauki...........Allah ya kyata ameen.

To fa makamancin wannan alamrinne yake faruwa ga dukkan matar da ta zama yar zuwa wajen bokaye da yan bori,da masu yin sihir,haka take faruwa da dukkan wanda yatare wajen yan bori,da bokaye sujefa mutum zuwa ga hallaka kuma suraba shi da uabangijinsa.Ta hanyar sa shi aikata miyagun ayyuka,wadanda Allah ya haramta.

Ubangiji Allah katsare mana imanin mu,katsare mu daga afkawa cikin hallaka,da hasara,da tabewa akan neman duniya,ya Allah kakara shiryar damu tafarki madai dai ci ameen.

SUWANE NE AZUMI YA WAJWBA AKANSU?

Wadanda azumi yazama wajibi akansu suyi shi sune kama haka:((Bisa tattaruwar maluma akan wannan cewa azumi ya wajaba ne akan mutum wanda musulmi,kuma mai hankali,kuma baligi,wanda yake lafiyayye,wanda yake kuma azaune agari))

Dan haka azumi bai zama wajibiba ga wanda yake da tabin hankali.

Azumi bai zama wajibi ba ga wanda bai balaga.

Bayan haka azumi yawajaba akan mata,amma banda macen da takeyin jinin haila,ko na haihuwa,lallai dole har sai yazama mace tana da tsarki,daga jinin haila ko na haihuwa.

Amma abinda yake tabbatar da cewa azumi ba wajibi bane ga wanda yake da tabin kwakwalwa, kuma baligi,bisa fadar maaiki saw.((Ana dauke alkalami abin rubutu akan mutane kwara (3)
(1)Ana dauke abin rubutu akan wanda yake mai tabin hankali.

(2)Ana dauke alkalami abin rubutu akan wanda yake yin barci,har sai lokacin daya falka.

(3)Ana dauke abin rubutu akan yaro karami har sai lokacin da balaga yafara mafalki.

Amma akace anso ga wanda yake majibincin wannan yaron ko mahaifansa da suyi masa umarni dayin azumi gwargwadon yadda zai iya domin ya koya,hakan kuma yin koyine da Sahabatu rasulallah.Domin sahabban manzom Allah swa.suna ummartar yaransu dayin azumi.

Ansamo wani hadisi daga Rabii dan Muawiz tace:Cewa manzon Allah saw.Akwai wata rana daakayi gari ranar ashura ya aika zuwa yan kunan alansar cewa((Duk wanda yawayi gari yana cin abinci to yacika sauran abinda yaragu na wannan ranar,wanda kuma yawayi gari yana azumi to yacigaba da azuminsa))

Bayan haka tace kuma Mun kasance munayin azumi,kuma yaranmu ma sunayi,muna sasu sunayin wasa amma da zarar muka ga yaro zaiyi kuka to sai muce yaci abinci sai muba shi abinci.

Bayan abinda yasa akace azumi yawajaba akan wanda yake lafiyayye kuma baligi,wanda zaune agari ba matafiyi ba shine,wannan ya kafune bisa fadar Allah swt.((Cewa wanda yakasance mara lafiya daga cikinku,ko wanda akan hanyar sa ta tafiya to zai iya ajiye azuminsa,amma zai gididdige kwanakin dayayi domin yin ramuwa agaba.

Amma idan mara lafiya yaga zai iya yin azumi,koko mata fiyi yaga zai iyayin azumi to wannan babu laifi hakan yayi,domin damar daaka basu na suci abinci wannan rangwamene akayi masu,domin saukaka masu,amma idan sunga suna iyawa to hakika sundauki aiki mai girma.

Wallahu taala aalam.

Ya Allah kabiya mana dukkan bukatun mu na alkairi,kayafe mana zunuban mu zahiri,da badini,manya da kanana kara bautar damu da samun jinkan ka,da rahamarka,awannan wata mai alabarka ameen.

Azumi yana daga cikin rukunnan muslunci kwara (5)

Alal hakika kamar yadda kuka sani azumi yana daya daga cikin rukunnan muslunci,kuma wajibi shi,domin yana daga cikin abubuwan wadanda muslunci ya wajabta.

Allah swt.yana fada acikin suratul bakra"Yaku masu imani hakika mun wajabta yin azumi akan ku kamar yadda muka wajabta shi ga alummar dasuka gabace ko kun kasance masu jin tsoron Allah.ayah(183)

Allah swt.yakara da cewa "Watan Ramadan shine wata wanda aka saukar da alqurani acikin sa domin yazama shiriya ga jamaa,da kuma hujjoji na shiriya da rarrabewa tsakanin abinda yake dai dai,da kuma wanda ba dai dai,tsakanin bata da kuma shiriya,tsakanin gaskiya,da kuma karya.....yakara da cewa dukkan wanda ya halarci wannan wata yana mai lafiya,yana mai hankali,kuma wanda yake baligi to ya azumce shi.bakra ayah(185).

Ansamo wani hadisi daga dan Ummar (ra)yace:Manzon Allah saw.yace:((Angina addinin muslunci ne abisa abubuwa kwara (3)

(1)Mutum ya shaida babu wani abu da ya cancanta a bauta masa sai Allah swt.shi kadai.

(2)Shine dole ka tabbatar cewa Annabi Muhammad saw.Manzon Allah ne.

(3)Kuma shine tsayar da sallah,maana kabatar da sallolin farilla.

(4)Da kuma bayar da zakka.Ga wanda Allah swt.yaba shi iko,da hali.

(5)Ziyartar dakin Allah,da kuma azumtar watan Ramadan.

Ansamo wani hadisi daga Abu huraira (ra)Yace:manzon Allah saw.Yace:Dukkan wanda ya azumci watan Ramadan yana mai imani,da kuma kyatata zaton sa ga Allah to Allah zai gafarta masa zunubansa da suka gabata.

Anrawaito wani hadisi shima daga Abu Huraira (ra)yace:Hakika maaikin Allah tsira da aminci su tabbata agare shi yace:Allah mai girma da daukaka yace:Kowanne aikin lada wanda dan adam zaiyi to nasane wannan,amma banda azumi,azumi wannan nawane,nine zanbada sakamakonsa da kaina.Azumi kuma kariyane,kuma garkuwane,yace idan aka wayi gari dayan ku yana azumi to kada yarika yin maganganu na alfahsha,maganganu marasa amfani,kada yarikayin ayyuka marasa amfani,ko wasanni marasa anfani,yace idan wani mutum yazage ka alhali kana azumi,ko yanemi da fitina,ko yane meka da fada to kace masa ni azumi nike,ka mai maita masa hakan har sau biyu.

Yace narantse da wanda rayuwata take a hannunsa yace warin bakin mai azumi awajan Allah ranar alkiyama yafi kam shin Almiski,kuma mai azumi yana da abubuwan farin ciki kwara biyu,wadanda zaiyi farin ciki dasu:Sune Alokacin da yayi buda baki zaiyi farin ciki da haka,bayan haka kuma da lokacin da ya hadu da  Allah swt.nan ma zai yi farin ciki da wannan azumin da yayi.

Domin akwai wani hadisi daaka samo daga Sahal dan Saad (ra)Yace:Hakika manzon Allah saw.yace acikin aljannah akwai wasu kofofi anace masu rayyan,wadannan kofofi masu azumine kadai zasu shigesu aranar alkiyama,babu wani mutum daya da zaa bari ya shiga wanda ba mai azumi ba.Yace zaarika yin kira ana cewa .......Ina masu azumi...ina masu azumi?Daganan zasu tashi babu wani mutum daya da zaa bari ya wuce wannan kofa sai su kadai kawai,kuma da zarar sun gama shiga sai arufe kofar bawanda zaa bari yakara shiga daga nan.

Ya ubangiji kasa muna daga cikin wadanda zasu shiga wannan kofar ameen.