Boka,da kuma malaman duba maganar gaskiya dukkansu sun kafurce ma Allah swt.saboda sunyin daawar sanin gaibi,abinda yake aboye ko zai faru jibi,nanda sati,shekara,ko shekaru,domin hakika sanin gaibi sai Allah.
Duk da cewa wasu maluma sukan kasa sanin gaibi kala daban,kamar alal misali Allah yakan sanar da annabawa wasu alamura ta hanyar wahyi daake yi masu.da dai sauransu.
Amma mafi yawa daga cikin gaibin da yan bori,da bokaye,da malaman duba suke daawar sanin sa badole bane yazama gaskiya,da yawa sunayin dubaru domin amsar kudin jamaa ne kawai wadanda suka rafkana,ta hanyar zana alkaluma,ko bugun ramli,kokuma duba hannun mutum,ko azuba ruwa a koko ko kwalba da sunan ganin matsalar mutum,koko madubi,da dai sauransu.
Domin bugun kasa duk da cewa irin harrufan alqurani ne ake bugawa suzama harrufa,to wannan ba dalili bane nayin haka,saboda ba shine manufar sanar da wannan ilimin ba,domin Allah swt.yace mun sanya ilimin hisabi ne,ba don ayi dubaba sai don kusan yawan kirgan shekaru,da kwanuka,da watanni.
Amma yanzu sai kaga anmai da abun sanaa,yanzu idan mutum yaje wajen neman magani,ko wata bukata in har wannan bokan,ko dan duban,ko dan bori bai iya wadannan dubarun ba,to bazai sami ko mai ba.......saboda tsabar imani da wasu daga cikin alumma dasukayi da hakan.
Kuma inda babbar illar take shine zaka gani sukan fahimci cewa menene kake so,to koda sunga cewa wannan abun ba zai yiwuba to bazaa taba fada maka hakaba,domin idan anfada maka gaskiya to bazaka bada kudi da yawaba,wannan dalili sai yasa afada maka karya domin kabada.
Kokuma koda anga cewa wannan bukata taka babu wata matsala zata yiwu sai ace kai ai dole sai anyi aiki akai,nanma afada maka karya kawai don a amshi kudinka,to wannan kuma ya shiga cikin saba ma Allah,domin yin karya haramunne a muslunci.Kaga daganan ata dalilin neman duniya mutum yazama makarya ci karfi da yaci.
Akwai wani babban mutum awannan kasar tamu da zan fadesa kowa zai san shi,domin yasami matsayi kala daban,daban wajen aiki,awani lokaci sai ya fito takara kuma yasa aka tara masa malamai irin wadannan masu yin duba din!!!
Kowa da ya buga kasa sai ai zaayi nasara babu makawa zai ci wannan zaben.
Sai wani malami shi kadaine yace aa gaskiyar magana babu nasara akan wannan tafiya,domin bazai ci wannan takaraba,yace kai karya kakeyi dukkan wadannan maluma kowa yace zaayi nasara sai kai kadaine zakace ba zaayi nasaraba,wannan ba gaskiya bane.
Saura aka basu buhunan shinkafa,da kudade masu yawa aka sallame su suka tafi.
Shi kuma da yace bazaayi nasara hakanan yata shi yatafi.
Anan nan anata yin kamfe akazo wajen yin zaben yan labai yafadi baiciba!!!Nan take yagane cewa sauran wadannan maluman karya suka fada masa kawai domin yabasu kudi.
Wannan dayan shi kadai ne yafadi gaskiya.
Domin manzon Allah saw.yace dukkan wanda yaje ma mace wanda take jinin haila maana yasadu da mace mai yin jinin haila,da kuma wanda yasadu da mace ta duburarta,da kuma wanda yaje wajen boka to yakafurta da abinda ka saukar agare shi.Allah yakare mu ameen.
Domin boka ko dan bori,ko malumin duba idan yafadi gaskiya sau daya to sai yayi karya sau( 99)Amma mutanen da suka rafkana zuciyar su ta dusa she bazasu gane hakanba.
Domin mutane suna zuwa wajen su domin sanin abinda zai faru agaba,da abin farin ciki,da kuma abun bakin ciki,imma tahanyar aure ko kasuwa,da bincike akan abinda yabata da dai sauransu.
Sannan kuma mutane sukan gaskta abinda aljannu suka fada abakin bokaye ko yan bori.Bil hasalima yanzu idan kana bayar da magani awajen wasu indai bawai kana da wasu shaidanun aljnnu dake ma wahyiba to basu dauka cewa kasan wani abu.Allah yakyata ameen.
Ban mantawa akwai sanda inayima wata baiwar Allah Ruqqa sai wannan aljanin yace ai shi yana kareta ne ,badon haka da abun yayi tsanani sosai!!!Sai nace masa kai wayake kareka yace Allah,nace to itama Allah ne yake kareta.......kuma nanu na masa hakan amma yakasa ganewa.
Daga nan nace masa tunda kaki yarda da abinda nafada to yanzu kasan abinda zai faru dakai anjima da yamma?yace aa,sai yace ai kaima baka saniba,nace masa dama kaji nace maka nasan abinda zai faru danine nanda anjima.
Nace masa dama kai da kake cewa kana kareta to kai kanka bakasan cewa menene zai faru dakai nanda anjima ba to tunda kau hakane to ta yaya zaka iya kareta.
Amma malamai sunce kamar alal misali wanda yatafi wajen su domin yin gwaji,amma shi bai gaskata suba cewa sunsan gaibi,amma yana zuwa domin ya gwada yagani,da dai sauransu to wannan airin haka bai zama kafuri ba,amma sai dai bazaa karbi sallar saba ta kwana (40)Dalili kuwa shine fadar maaiki saw.cewa dukkan wanda yaje dan duba ya tambaye sa akan wani abu,to bazaa karbi sallar saba har ta kwana (40)Tare da cewa wajibine kuma yaci gaba da yin salla,kuma yana tuba zuwa ga Allah swt.
Wallahu taala aalam.
Ciyarwa acikin watan ramadan ta hanyar dafa abinci abayar da sadaka,ko kuma taimaka ma bayin Allah abasu sudafa da kansu yanada lada mara iyaka.Domin fadin Allh swt.acikin suratul bakra.cewa:(Misalin mutunen da suke ciyar da bayin Allah don Allah,to kamar misalin mutumin daya shuka kwara dayane ta dawa,ko masara,ko gero,wannan kwara dayan daya shuka tafito tayi tushe (7)kuma kowanne tushe yayi kwaya dari ba kwai(700)To kamar hakane ubangiji yake rubanya lada ga wanda yaciyar domin ko yabayar da sadaka,kuma Allah swt.yace yana kara rubanyawa ga wanda sama da (700)din ga wanda yaso))
Ya Allah kabamu abinda zamuyi,kuma kabamu ikonyi ameen.
No comments:
Post a Comment