Mace mai ciki,da kuma wanda take shayarwa maluma sukace idan bazasu iyayin azumi ba,kokuma suka ji tsoro ga yaronsu to suci abinci,amma zasu bayar da fansar wannan azumin,kuma babu ramuwa akansu.
Ansamo wani hadisi daga dan Abbas (RA)yace:((Anyi rangwame ga wanda yake tsoho,da kuma mace tsohuwa awajan wannan,amma abinda yake akansu shine suci abinci kuma suciyar akowacce rana zasu ciyar miskini.Babu ramuwa akansu.wanda yake ada koda tsoho ko tsohuwa zasu iyayin azumi idan sunso suyi azumi,idan sunso suci abinci,sai suciyar da miskini akowacce rana sai aka shafe wannan da fadin Allah swt.cewa (Duk wanda yazama watan Ranadan yakama yanada cikakkiyar lafiya,da hankali,kumA baligi yazama wajibi yayi azumi))
Amma sai akayi rangwame ga mutumin dayake tsoho,ko mace tsohuwa idan basa iya yin azumi,da kuma mace mai ciki,da kuma wanda take shayarwa idan sunji tsoron cutarwa ga yayayan su to akace suci abinci,amma kowacce sai suciyar da miskini.
Bayan haka da kuma wani Karin bayanin daga dan Abbasu (RA)Yace ((Idan mace mai ciki taji tsoro akanta kada tasha wahala mai tsanani,da kuma mace mai shayarwa taji tsoro ga yaronta kada kada yasha wahala acikin watan Ramadan tahanyar rasa nonon da zai sha sai yace:to ya halatta suci abinci,kuma suciya da miskinai akowacce rana,kuma bazasu rama wannan azumin ba.
Ansamo wani hadisi daga Nafiu(RA)yace:((Wato yakasance wata diya daga cikin yayan dan Ummaru (RA)tana karkashin wani mutum bakurai she,kuma yazama tanada ciki acikin watan Ramadan,sai kishi yasame ta acikin wannan wata,kishi matsananci,sai dan Ummar ya ummar ceta dacewa taci abinci,kuma taciyar da miskini akowacce rana))
Wallahu aalam.
Ya Allah kagafarta mana zunubanmu gaba daya,kayi mana rahma,kabiya mana bukatunmu na alkairi ameen.
No comments:
Post a Comment