Sune kamar haka:
(1)Nafarko shine yin Sihir.
(2)Nabiyu kuma shine Bokanci.
(3)Shine arrafa maana Yan duba.
Alal hakika yin sihir kafurcine,domin yana kafurta mai yinsa domin yana daya daga cikin abubuwa kwara (7)wadanda maaiki Allah tsira da aminci yace Allah ya gaggauta ukuba ga masu yinsa,domin sihir yana cutar wa,baya da amfani((Domin Allah madaukakin sarki yana cewa suna neman sanin abinda zai cutar dasu,kuma bazai amfane suba))Suratul bakara (102)Bayan haka Allah swt.yace :Masu yin sihir bazasu kubuta ba takowacce fuska.Dahaa ayah(79)
Bayan haka mai yin sihir ya tabbata kafiri domin Allah swt.yana cewa((Annabi Sulaimana (As)bai kafurtaba,sai dai Shaidanune suka kafurta domin sune suke koya ma mutane yadda akeyin sihir,Allah swt.yace kuma babu abinda aka saukar akan wasu mutane kwara biyi haruta,da marut,balantana har su koyar da wani mutum daya sihir,sannan suce masa mufa fiti nane,don haka kada ka kafurta)).
Hukuncin mai yin sihir,shine kisa bisa zancen maluma,kuma dukiyarsa haramunce.
Don hakane zakaga daga cikin wasu jamaa wadanda suke jahilai,ko kuma azzalumai,ko wadanda suke masu raunin imani,suna zuwa wajan masu yin sihir domin suyi masu sihir,domin su aikata wani mummunan aikin taadanci akan wasu bayin Allah,ko kuma daukar fansa.
Akwai kuma wadanda zaka ga suna zuwa su aikata wata alfahsha,koko wani aiki wanda Allah ya haramta tahanyar dalilin zuwan su wajen wannan mai yin sihir din,ko don warware sihir,ko kuma neman duniya,ta hanyar jefa mutane cikin zinace xinace,ko aikata manyan kabair,kamar yin luwadi da sunan samun duniya,kokuma kashe rai duk da sunan neman duniya,domin balain da mai sihir yake haifarwa yafi balain daake haifar wa agidan giya.
Kokuma war ware sihir,ta hanyar sihir wanda wannan badai dai bane,domin baa warkar da cuta da cuta,sai dai awarkar da cuta da magani,tahanyar komawa ga Allah swt.da neman waraka agare shi,tahanyar karanta alqurani da dai sauransu.
Bana mantawa wani abin tada hankali,kuma babban balin da ya zama ruwan dare ayanzu ubangiji Allah yamana tsari kuma shikare mu ameen.
Wato akwai wata baiwar Allah da mai gidanta yake shirin kara sabon Aure,kuma yake dauko wanda zai aura din yana kawota har gida,har wata rana takira wannan matar tasa take ce mata wlh.idan nashigo wannan gidan dole sai kinbar shi,hakan yatada mata da hankali,hakan yarika jawo matsala a tsakanin ta da mai gidanta,akoda yau she sai dai nanuna mata girman Allah,da kuma tayi hakuri,tayi fatan alkairi,kuma tagaya ma ubangiji da muwar ta,har nace nima zan tai maketa da aduah akan samun zaman lafiya.........Ashe gaba daya hakan bai gam she taba......wlh har sai da aka wayi gari wata kawar banza tajata takai ta wajen wani makiyin Allah,da manzon sa saw.
Sai tafada masa dukkan da muwar ta akar she shine ya ummar ceta da cewa ta kwabe kayan jikinta duka saboda akwai maganin da zaayi mata,amma sai yaduba jikinta tukunna......Ya Allah kakare mu daga sharrin zamani ameen.
Bayan sundawo ne takirani take shai da man cewa itafa tayi wani abu amma bata san yazata yiba,bata san yazatayi tatubaba tafa she da kuka.........Daganan taka she wayarta,tun safe har zuwa yamma,daganan takara kirana tace wallahi malam wata kawata takai ni wajen malami ashe boka ne ban saniba,yace man nayi kaza da kaza.......Daganan takara fashewa da kuka!!!
Inna lillahi wainna ilaihi rajiun.
Daganan jikina ya hau bari,zuciyata takama makyarkyata.
Tace yanzu don Allah malam yazanyi natuba?Nace mata abinda yace kiyi kinyine tace aa,nace indai har bakiyi abinda yace kiyiba to da sauki...........Allah ya kyata ameen.
To fa makamancin wannan alamrinne yake faruwa ga dukkan matar da ta zama yar zuwa wajen bokaye da yan bori,da masu yin sihir,haka take faruwa da dukkan wanda yatare wajen yan bori,da bokaye sujefa mutum zuwa ga hallaka kuma suraba shi da uabangijinsa.Ta hanyar sa shi aikata miyagun ayyuka,wadanda Allah ya haramta.
Ubangiji Allah katsare mana imanin mu,katsare mu daga afkawa cikin hallaka,da hasara,da tabewa akan neman duniya,ya Allah kakara shiryar damu tafarki madai dai ci ameen.
No comments:
Post a Comment